26 Yuli 2020 - 11:14
An Aibata Shirun Da MDD Take Yi Dangane Da Mummunan Halin Da Mutanen Kasar Yemen Suke Ciki

Kakain majalisar koli ta kare hakkin bil’adana a kasar Yemen ya ce yana mamakin irin shirun da MDD ta ke ci gaba da yi dangane da mummunan hali na rashin makamashi da abinci a kasar ta Yemen.

ABNA24: Tashar talabijin ta Almasirah ta nakalto Tal’at Sharjabi yana fadar haka a wata hira da ta hada su. Sharjabi ya kara da cewa majalisarsa ta aika wasiku zuwa hukumomi daban-daban wadanda suke aiki da MDD danggane da rashin makamshi da kuma abinda a kasar Yemen amma sai shiru kake ji.

Kakakin majalisar koli na kare hakkin nbil’adama na kasar Yemen ya ce har yanzun kasashen saudiya da EAU suna ci gaba da tsare jiragen ruwa dauke da makamashi na kasar ta yemen. Ya kuma yi gargadin cewa idan har makamashi ya kara a kasar to kuwa kasar zata fada cikin mummunan hali.

342/